Majalisar Dattijai ta alaƙanta taɓarɓarewar barukokin Ƙasar nan, da yaƙi da ta’addanci da ƴan bindiga daɗi.
Kwamitin Majalisar akan lamurran soji ne ya bayyana haka bayan ya ziyarci wasu barukokin soji a Jahohin Filato da Bauchi domin gudanar da wasu ayyukan kwamitin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Jiga-jigan Siyasa kuma ‘Yan Kasuwar Jihar Sokoto, Sun Buƙaci Yahaya Bello Ya Tsaya Takara a zaɓen 2023
Shugaban Kwamitin Majalisar Sanata Ali Ndume yayin zantawa da Manema labaru yayin ziyarar, yace kuɗaɗen da aka ware domin ayi amfani dasu wajen gyaran barukokin, an yi amfani dasu domin biyan alawus-alawus na sojoji dake yaƙi da matsalar ta’addan ci a Najeriya.
Ya bayyana cewa majalisun guda biyu zasu yi bakin ƙoƙarin su domin ganin cewa an samar da ƙarin kuɗaɗe da za’ayi amfani dasu wajen gyara tsaffin barukokin soji tare da gina wasu.
Ya ƙara dacewa, an sanya sojoji gudanar da yaƙi wanda kamata yayi ace yan sanda ko wasu jami’an tsaro ke gudanar dashi.