Dole Mu Kori APC Daga Najeriya Idan Munason Mudaina Shan Wahala, Wike
Gwamanan Jahar Rivers Nyesom Ezenwo Wike yace wannan kangin da Yan Najeriya ke ciki zaisa su dole sai sun Kori Jam’iyyar APC daga Mulki a shekarar 2023.
KARANTA:-Dole A kama Sheik Gumi, Inji Femi Kayode
Gwamanan ya bayyana hakane lokacin da yake kaddamar da wani aikin hanyar da yayi a Port Harcourt a ranar Juma’a, wanda wani tsohon Dan majalisa yayi.
Wike yace irin wannan takurawa da sukai kan kafofin sada zumunta a wannan lokaci ya bayyana irin gazawa na gwamnatin.
Gwamna Wike yace babu wani irin salo na yaudara da za’a zoma Yan Najeriya don a sake yaudarar su, don bazasu amince da wannan yanayi ya cigaba ba.
Yace Kasar Najeriya tanada bukatar addu’oi don ganin an fita wannan kangin, ba hakan mukaso ba amma duk lafin gwamnatin ne,.
Sun fito kafafen yada labarai da sada zumunta daukar mu zasuyi abun azo a gani shiya muka zabesu a shekarar 2015, amma kuduba kuga irin halin da muka tsinci kanmu a yau, zaku basu dama suyi amfani da kafafen yada labarai da sada zumunta wajan yaudarar ku?, Dayawa daga cikin Mutane masu anfani da kafafen sada zumunta basa jindadin su.
Wike yace a halin yanzu jam’iyyar PDP ne kawai mafita ga Yan Najeriya. Yace idan Kuma Yan Najeriya suka sake karambanin zaben APC a 2023 to lallai kun hallaka kanku.
Daga karshe gwamanan ya gargadi masu manya Motoci dasu daina tsayawa a kan sabuwar hanyar da aka kammala ba, idan Kuma sunki gwamnatin jaha zata dauki mataki kansu.