Dole mu sake gina Fatan Ƴan Najeriya — Fayemi ya gayawa APC
Gwamnan Jahar Ekiti kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni na Najeriya Kayode Fayemi yayi kira ga Jam’iyya mai Mulki ta APC data tashi tsaye domin yin Gaggawar sake gina Fatan da Ƴan Najeriya ke garesu ta hanyar magance rashin cigaba, rashin haɗin kai da matsalar tsaro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: Zamu yi amfani da wasanni wajen Magance Talauci — Ministan Buhari
A lokacin da yake yabawa akan nasarar da Jam’iyyar ta samu tun lokacin da ta karɓi ragamar mulki daga Shekarar 2015, yace har yanzu akwai matsaloli dake fuskantar Ƙasar nan.
Yace matsalolin da suka haɗa da rashin tsaro, da matsalar tattalin arziki, ya ɓatawa Jam’iyyar shirin ta na magance matsalar rashin aikin yi.
Fayemi yace zai ɗora daga nasarar da Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tayi, idan har aka zaɓe shi a Shekarar 2023.
“Domin jaddada matsayar mu na Jam’iyyar data fi kowace, da kuma cigaba da samun goyon da mutuntaka daga ƴan Najeriya, zan yi dukkanin abinda zan iya domin magance matsalar tsaro, rashin aikin yi, Talauci, rashin dai-dai to, abinda ke neman hana ɗorewar zaman lafiya da rashin bin Doka.
Comments 1