Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hukunta wadanda suka samar da gurbataccen kaya bisa irin laifin da suka aikata.
Martanin Shugaba Buhari ya biyo bayan rahoton shigo da gurbataccen man fetur Najeriya.
Shugaban, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce an bayar da umarni ga hukumomin gwamnati da su bi duk wani mataki da ya dace da dokokin kasar don tabbatar da mutuntawa da kare masu sayayya daga cin zarafi na Yan kasuwa da kuma rashin adalci a cikin al’umma.
Umurnin yana mai da martani ne kan batun karancin albarkatun man fetur da ke da nasaba da gurbataccen Man Fetur din da aka shigo dashi daga kasashen waje zuwa kasuwannin Najeriya.
A cewar fadar shugaban kasar, kare muradun ingantattun kayayyakj shine babban abun fifiko ga gwamnati mai ci, kuma a shirye take ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare masu amfani da kayayyaki masu hadari, hasarar ko jikkata daga amfani da kayayyakin da ba su da inganci.
Idan za’a iya tunawa cewa, An Sami rahoton shigo da man fetur da ake amfani da shi a cikin gida, sama da lita miliyan 100 na gurbataccen zuwa kasuwannin Najeriya, lamarin da ya janyo karancin man fetur a yayin da hukumomin gwamnati suka yi kokarin kawar da gurbataccen man daga kasuwannin.
Comments 1