By Abbas Yakubu Yaura
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya shaidawa ‘yan kwangilar dake tafiyar da aikin gina layin dogo na Kaduna zuwa Kano dasu kammala shi a farkon rubu’in shekarar 2023.
Ya bayar da wa’adin ne a Kano ranar Alhamis yayin da yake duba aikin.
“Muna nan ne don gano ko CCECC ta fara aiki da kuma nisan da suka yi, Domin suna da burin kammala wannan abu a karshen shekara mai zuwa ko kuma a cikin rubu’in farko na sauran shekara”.
“Ya zuwa yanzu ganin ana yin wannan kafa bai isa mu yi suka ba tukuna sai lokacin da muka fara sauran sassan aikin.
“Ba mu da wata matsala ta biyan diyya a wannan hanya, Kafin mu fara, mun tabbatar da cewa an biya kowa albashi kafin ma mu fara sharewa kuma wannan shi ne abu na farko kan dabarun aiwatar da aikin.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ministan yace kwangilar ta shekara uku ce kuma yana ingizawa ne domin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da ita kafin ya bar mulki.