Hukumar hulɗar al’amuran jama’a ta CAC ta bayyana cewa ba gudu ba ja da baya dangane da sabon tsarin da ta shigo da shi akan kamfanunuwa da kuma masana’antu, duk da ƙorare-ƙorafe da mutane ke yi.
Hukumar tace tana jiran sahalewar majalisa ne kafin ta fara ƙaddamar da sabon shirin.
Hukumar tace shirin ya samu sahalewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kuma yana ɗaya daga cikin nasarorin da yake ganin za a saka a cikin jerin nasarorin shugaban.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-an-saki-shugaban-kungiyar-can-reshen-jihar-nassarawa/
Ma’ajin hukumar Alhaji Garba Abubakar, ya bayyana mamakinsa game da yadda wasu suke sukar tsarin musamman ma Majami’u da kuma ƙungiyar mabiya addinin kirista ta CAN.
“Daga yanzu dole suke fitar da rahoton yadda suke samu da kuma kashe kuɗaɗen coci-coci, kuma dole su turo wa hukumar CAC”, cewar ma’ajin.
Ya ƙara da cewa wannan tsari ya shafi dukkanin wata ƙungiya ta addini da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.