Daga Sulaiman Musa
Tsohon dan takarar shugaban Nijeriya, Kingsley Moghalu, ya mara baya wa kiranye-kiranyen sai Ministan sadarwa, Isah Ali Pantami ya yi murabus daga wannan mukamin nasa bisa ra’ayinsa na baya da ya goya wa ‘yan ta’adda baya.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tweeter, Moghalu ya bayyana cewar bai dace Pantami ya cigaba da zama a matsayin ministan Nijeriya ba.
Ya ce, ba laifi ba ne mutum ya yi laifi a baya amma ya gane ya kuma tuba kan abun da ya yi a da baya, “Amma da zarar hujjoji suka fito da suka nuna wani minister da ke ci ya taba nuna goyan bayansa ga kungiyoyin ta’adda, bai dace ya cigaba da zama a kan kujerarsa ta minister ba sam-sam,” inji shi.
Ya kuma nuna adawarsa kan tsoma baki da gwamnatin tarayya ta yi na cewa tana bayan Pantami, ya bayyana cewar sam hakan bai dace ba.