Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin tarayya kan abin da ya bayyana da almundahana da dukiyar al’umma.
A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis din nan, ya shawarci gwamnatin da ta daina tura jami’an gwamnati horo a kasashen waje da kudaden masu biyan haraji yayin da ma’aikata a jami’o’in gwamnatin kasar ke yajin aiki.
A cewar dan takarar shugaban kasar, ya kamata gwamnati ta daina karkatar da abubuwan da za a sa a gaba, ta kuma tabbatar da cewa ba a yi watsi da matasa wadanda su ne makomar al’ummar kasar nan ba.
“Dalibanmu da shugabanninmu na gaba suna zaman banza a gida ko a wasu wuraren da ba a so, yayin da gwamnatinmu ke kashe miliyoyin kudade a kasashen waje, wanda ake zaton horar da masu rike da mukaman gwamnati a jami’o’in Ivy League a fadin duniya,” in ji Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/tsohon-minista-ya-bukaci-kotu-ta-kori-tinubu-atiku-daga-takarar-shugaban-kasa/
“Ta hanyar irin wannan sakarci na siyasa, muna haifar da rashin sanin yakamata a cikin al’umma wanda wata rana za su shiga cin kasuwa tare da daukar fansa a kan al’ummarmu. Dangane da shugabanci na gari, irin wannan horon da ake daukar nauyinsa da kudaden jama’a ya kamata a tsaya nan da nan, har sai dukkan makarantunmu sun fara aiki yadda ya kamata.”
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ma’aikatan jami’o’in da suka hada da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU), kungiyar ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba(NASU), da kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT), sun shiga yajin aikin saboda dalilai daban-daban.
A ci gaba da yajin aikin da aka dade wanda ya gurgunta harkokin ilimi a jami’o’in sama da watanni biyar, jami’an hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC) sun halarci wani babban shirin jagoranci na Makarantar Kasuwancin Judge (JBS) a Jami’ar Cambridge ta kasar Birtaniya.
Shi ma kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya sha suka da kakkausar murya kan wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta na baya-bayan nan inda ya yada hotunansa na daukar kwas a jami’ar Harvard.
Obi, ya jaddada cewa idan har ana bukatar irin wadannan horaswar, ya kamata a rika gudanar da su a cikin kasar kawai.
(CHANNELS TV)