Kungiyar Dattawan Kiristocin Kogi ta Gabas, (KECEF) ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), da ta nuna gaskiya a zaben 2023 mai zuwa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Dattawan wadanda suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar da suka fitar a Kaduna a karshen taron addu’o’in ta na kasa, sun kuma bayar da shawarar wayar da kan masu zabe a tsakanin masu zabe kafin ranar zabe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa: Sarkin Musulmi Ya Fadawa Yan Najeriya Mafita
Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da baiwa wani addinin guda tikitin takara da wasu ‘yan siyasa da jam’iyyun siyasa suka yi.
Dattawan sun kuma ce saboda tabarbarewar tsaro a kasar nan, suna gargadin matasa Kiristoci da masu neman ofishin siyasa da su guji tashin hankali ta kowace fuska.
Kungiyar ta jaddada bukatar da ke akwai na dukkan dariku da sauran kungiyoyin da suke da alaka da su da su kara yin addu’a domin samun zaman lafiya a Nijeriya.
Dangane da ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Kogi a kwanakin baya, Dattawan sun nuna matukar damuwa da halin da al’ummar jihar ke ciki, don haka sun yi kira ga mahalarta taron da sauran jama’a da su bayar da gudummawar kyauta ga asusun wadanda ambaliyar ta shafa da za a taimaka musu.
A cewarsu, kungiyar na shirin bayar da tallafin Naira miliyan Goma ga wadanda abin ya shafa.
A WANI LABARIN KUMA: PDP Ta Tafka Asara, Jagororin Jam’iyar Biyu A Yobe Sun Koma Jam’iyar APC
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni Ya tarbi Hajiya Musafaram tsohuwar jagora a Jam’iyar PDP da ta sauya sheka daga jam’iyar zuwa APC mai mulki a Jihar.
Daraktan Janar na yada labarai da kula da harkokin kafafen yada labaran Gwamnan Mamman Mohammed ne ya bayyana hakan acikin wata sanarwa da ya fitar