Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaici da ɓacin ransa matuƙa bisa kisar tsohon mai baiwa shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmad Gulak.
A jiya Lahadi ne aka hallaka Gulak a birnin Owerri na Jihar Imo to amma har kawo yanzu ba a gano su wanene makasan ba, ko da yake an alakanta kisar tashi da ƴaƴan Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB.
Amma nata bangaren, IPOB ta ce sam ba ta da hannu ko masaniya kan wannan mummunar al’amari.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai tsllafawa shugaba kan yada labarai Mallam Garba Shehu ya fita, ta ce shugaba Buhari ya harzuka matuka kumaba za a taɓa barin Gulak ya tafi a banza ba.
“Bari na faɗa da babbar murya cewa, duk mai hannu cikin wannan aika-aika dole ne ya girbe abinda ya shuka, domin nuna kasa ce ta doka” Cewar Sanarwar.
Mutuwar ta Gulak ta zo daidai lokacin da shugaban kungiyar Inyamurai ta IPOB Nnamdi Kanu ya bada umarnin ci gaba da zama a gida a yankin na kudu don nuna alhini da abubuwan da ya ce an yi wa mazan jiyan yankinsu.