Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu ya bayyana cewa; babu wata suka da zai sanya su sassauta akan yunkurin kafa dokar yiwa kafafen watsa labarai garambawul a Nijeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a yayin zaman da ya gudana tsakaninsa da kafafen watsa labaran Intanet a Legas. Lai ya tabbatar da cewa; za su tabbata da sun dabbaka shawarwarin da aka bayar na amfani da kafafen yada labarai.
Lai ya ce marasa kishin kasa ne kawai da masu kama karya za su ki amincewa da dokar da zai yaki labaran boge da kalaman batanci musamman a cewarsa a kafafen yada labarai na gidajen rediyo da Talabijin. Lai ya ce wadanda suka san me suke yi, ba za su yiwa dokar zagon kasa ba, domin a cewarsa ba su da abin da za su yi fargaba a kai.
Lai ya ce wannan ba mataki ne za su dauka na dakile ‘yancin fadar albarkacin baki, ko takurawa wani ba, sai dai ya ce; masu yada labaran boge da kalaman batanci su kadai ne kawai ba za su yi bacci ba dangane da dokar.