Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson yana can yana wani yunkuri na tilasta yin rigafin Korona ga kowace ƙasa.
Johnson ya ce zai gabatar da wannan bukata ce a yayin taron Manyan kasashe masu tattalin arziki na G7 a birnin Landan na Birtaniya.
Wannan taro shine zai kasance na farko da za a yi keke da keke tun bayan ɓullar cutar Korona, kana ziyara ta farko ga shugaba Joe Biden zuwa Birtaniya tun bayan ɗarewarsa karagar mulki.
Kasar Amurka ta kuduri aniyar samar da rigafin Korona kimanin miliyan tamani ga kasashen da fatara ta yi musu katutu, yayin sauran ƙasashe bakwai dake da karfin tattalin arziki kuma za su samar da kasa da haka.
Ko da yake har yanzu Birtaniya da Canada ba su fadi adadin allurar da za su bayar ba, sai dai ana ganin a yayin taron, Boris Johnson zai bayyana nawa kasarsa za ta bayar.