Tsohon Gwamnan Jihar Osun Prince Olagunsoye Oyinlola ya ce tilas ne Jam’iyyar PDP mai adawa ta hada kai don ceto Yan Najeriya daga halin kunci da APC ta jefa su ciki.
Tshon Gwamnan ya bayyana wannan amanna ne a yayin da Tsohon Mataimakin gwmnan Jihar Oyo Taofeek Arapaja da kuma magoya bayan shi suka ziyarce shi a gidan shi dakebirnin Oshobo ya ce idan har PDP ta hada kai to lallai babu makawa za ta doke APC a babban zaben 2023.
“Abinda ke kai ga nasara a lamura shine hadin kai, kuma na tabbata idan muka hada kan mu to babau makawa za mu chaske jam’iyya mai ci a babban zaben 2023”
“Gwamnatin APC ta gaza akowane bangaren shugabanci a kasar nan, to amma idan mutum zai yi son zuciya to zain iya cewa ta cika alkawuran da ta dauka yayin yakin neman zabe”.
Tsohon gwamnan ya bayyana gamsuwar shi da yadda al’amura ke gudana tsakanin tsohon gwmanan Ekiti Ayo Fayose da kuma Sanata Abiodun Olujinmi bisa yadda suke samun fahimtar juna tsakkanin su kan zaman doya da manja da suka dade suna yi.