Gwamnonin jihohin kudancin Nijeriya 17 sun bayyana goyan bayan su da hukuncin kotun Jihar Rivers wanda ya baiwa jihar damar karbar harajin VAT maimakon gwamnatin tarayya, tare da bukatar ganin shugaban Najeriya na gaba ya fito daga yankin su.
Wannan matsayi ya biyo bayan taron da suka gudanar yau a garin Enugu wanda ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi tsaro da tattalin arzikin da kuma siyasa.
Taron wanda ya gudana a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yaba da yadda jihohin yankin kudancin kasar ke aiwatar da dokar hana yawon kiwo wanda aka fara amfani da ita a wasu jihohi tun daga ranar 1 ga wannan wata na Satumba, yayin da taron ya bukaci jihohin da basu riga sun amince da dokar hana kiwon ba da su gaggauta yin haka.
Taron ya kuma bukaci amfani da jami’an tsaro na shiya da kuma bukatar tintiba da hadin kai a tsakanin su tare da musayar bayanan asiri domin kare lafiyar jama’a da dukiyoyin mazauna yankin kudancin kasar.
Yayin da gwamnonin suka sake jaddada bukatar su na sauya fasalin zaman tarayyar da ake amfani da shi yanzu haka a Nijeriya, sun kuma sake bayyana matsayin su na ganin shugaban kasar da za’a zaba a shekarar 2023 ya fito daga kudancin Najeriya domin tabbatar da adalci ga kowanne sashe na kasa.