Kudri na hudu Cikin Kudirorinsa shine kan kananan Yara
An gabatar da wannan kudirin ne, a wani yunkuri ko mataki na tabbatar da ganin an ba rayuwar kananan yara mahimmanci a cikin al’umma, bayan an haife su, tare da tabbatar da ganin sun cimma muradan cimmawa wanda kuma tuni Kudirin ya tsallake karatu na 1 a zauraren majalisar dattawan.
SAI KUMA KUDIRIN MALLAM UBA SANI NA 5
5. Kudrin Kwalejin Bincike Da Kimiyyar Gandun Daji A Birnin Gwari (2019)
An gabatar da Kudirin ne, musamman don ganin an fadada ilimin sanin mahimmancin gandun daji a Nijeriya. Idan har wannan Kudirin ya zama doka, to al’ummomin yankin za su kara samun kusanci da gwamnatin tarayya, sannan a samar da guraben ayyukan yi, ta yadda za a magance matsanancin talauci a cikin al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matawalle ya Kori Manyan Masu taimaka mishi
Haka kuma, zai bada gagarumar gudunmuwa ta fuskar samun kudin shiga.
SAI KUDIRIN MALLAM Uba Sani NA 6
6. Kudirin Jami’ar Kimiyya A Kaduna ( 2019)
Kudirin ya bukaci a sauya Kwalejin Kimiyya da Fasa ta jihar Kaduna zuwa Jami’a, kuma an gabatar da shi ne, ta yadda hakan zai bada gudumuwa wajen samar da kwararrun ma’aikatan da ake bukata a masana’antu, tuni shi ma wannan kudri ya tsallake karatu na 1 a zauren majalisar dattawan ta Nageriya.
Sanata Uba sani shine Sanatan Dake wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya, kawo yanzu dai, Sanatan ya gabatar da Kudirori har guda ashirin 20, Tsawon zuwan shi majalisa na Shekaru biyu, Kudirorin nasa baki daya suna da nasaba ga taimakon Al’ummar da yake wakilta tare da, sauran Al’ummar Nageriya baki daya.