• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, February 6, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

Domin Magance Aikata Fyade, A Rika Yankewa Masu Dabi’ar Mazakutarsu –Dakta Bashir

said by said
July 28, 2020
in Labarai
Reading Time: 4 mins read
1 0
0
1
SHARES
9
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Mai karatu wannan ita ce cikakkiyar tattaunawar da wakilinmu Yahaya M Abdullahi ya yi da daya daga cikin Malamai a babban Jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi, wato Dakta Idris Bashir Abdullahi wanda ya kasance daya daga cikin masu fashin baki na yau da kullum kan al’amuran siyasa da karatu a jihar Nasarawa. Wakilinmu ya zanta da shi ne bayan kammala jawabin da ya yi a dakin taro na Jami’ar NSUK bayan gudanar da gagarumin taro akan kare hakkin yara kanana wadanda ake yi musu fyade a fadin jihar Nasarawa dama kasa baki daya. Asha karatu lafiya.

Yanzu ana lokaci ne na take hakkin Yara mata ta hanyar yi musu Fyade, ko Ya ya Dakta yake kallon wannan lamarin?

 

Harkar Fyade wani abu ne wanda Malamai a makaranta da sauran manyan mutane a kasa sun yi rubutu akan fyade, wato shi fyade abu ne da ake yi da karfi kuma ba sai ga mace ba, a yanzu har namiji ana masa fyade amma abin da muke so mutane su gane shi ne, fyaden da ake yi yanzu ya canza kamanni ya zama wani abu daban, yanzu manya ne ke yi da kananun yara, Yara ‘yan wata biyu a duniya ko kuma ‘yan shekara uku a duniya za ka ga ana yi musu Fyade, to wannan magana na fyade dole mu zauna mu duba mu gani cewa, shin mene ne salsalar da yasa ake aikata wannan aika-aikar na fyade?

Wasu sun ce halin kulle ne da ake ciki wato ‘lockdown’ alhalin ba shi bane, idan rashin aiki ne zai sa ka yi fyade ai lokacin da ake aiki nan ma ana fyade, abin da zamu yi la’akari da shi shi ne, mu duba abubuwa makamancin haka, wadanda suka yi rubutu suna cewa abin da kesa fyade shi ne wanda ake musu fyade in ya zamanto ba a kula da su. Misali namiji ya ga yarinya karama kyakkyawa tana tafiya a cikin yanayi mai kyau tana ta yawo a Unguwa, ka ga wannan zai iya mata fyade saboda ya ganta a waje ba kula, amma idan tana cikin gida fa? Ya kamata mu duba wannan lamarin nan ma mu dunga killace yaranmu a gida ka da mu dunga barin su suna yawo ba tare da mun san ina suke zuwa ba.

 

Na biyu kuma abin da yake firgitar damu a wannan lokacin in ka duba ka ga irin kananan yaran da ake ma fyade, abin da za ka tambaya shin wadanda suke aikata wannan aikin na fyade shin ba su da hankali ne ko kuma wani ciwo ne na hauka yake so ya kama su? Abin da zamu duba mu gani, Ni a nawa tunanin, yanzu abun ya zama na hauka domin kuwa ya kamata mu dunga duba abubuwa biyu, na farko shi ne wanda na fada maka cewar rashin kulawa da yaran da ake musu wannan aikin, har yanzu hukumomi ba su hukunta wadanda aka kama su da wannan laifin ba, shiyasa wanda zai yi wannan aikin zai duba ai ba a hukunta wanda ya yi na baya ba ko kuma ai da na yi a baya ma ba a min wani hukunci ba saboda tunda babu wani hukunci to nima zanyi na ji ko kuma zan sake aikatawa in ya zamanto mai aikatawar ne, amma abin da muke so a yi la’akari da shi a nan shi ne, abu ne da ya kamata a ce ba wai kawai hukuma ne za ta yi ba, kowa yana da rawar da zai taka a wannan lokacin tun daga dan Sanda har kan Gwamna, ya kamata a zauna a duba idan ma za a yi doka ma masu aikata wannan mummunan aika-aikar ya kamata dokar ya zamanto tsakaninmu ne daga cikinmu.

Akwai wani Malami yana karantarwa a bangaren Shari’a ya ce in zaka yi magana akan hukunci zaka yi ne da yanayin jama’ar da kake tare da su, in ka yi dokar da bai shafi mutanen wajen ba ba zai yi tasiri ba. Kamar yanzu misali ka dauki dokar Keffi ka yi aiki da shi a Kano ba zai yi aiki ba, sai dai ka yi dokar Keffi da Keffi kawai, to ya kamata a duba wannan maganar na fyade, Iyaye su gaya ma yaransu ga matsalolin dake faruwa, wannan lamarin ya wuce  maganan mutum ya yi domin ya ji dadi magana ne na wani abu daban wanda ba wanda ya sani sai wanda ya aikata hakan

Ko akwai wani Shawarar da Dakta zai bama Gwamnati kan masu aikata wannan aika-aikar?

Shawarata ga hukuma idan an kama masu irin wannan mummunan aika-aikar, kafin ma a zauna a ce an kaddamar da wannan dokar, ni shawarar da zan bayar shi ne kawai a yanke masa mazaqutarsa in dai in aka yanke zai rayu to kawai a yanke masa din, idan kuma ba zai rayu ba to a kashe shi kawai shi ne babban abin da za a yi domin maganin wannan mummunan aika-aikar.

Daga lokacin da aka kama shi ana kai shi to kawai a aikata masa wannan aikin na hukunci ko a kashe shi, ko kuma a yanke masa Mazaqutarsa kawai, ka da ma a saka masa bindiga, a yi amfani da bangaren rataya a rataye shi, a fito da shi kuma a fili gaban jama’a kowa na ganin irin hukuncin da ake yanke masa komai kudinsa kuwa, komai iyalansa, in ka duba sauran kasashen duniya za ka ga duniyar mutum bai hana a yi masa hukunci akan abin da ya aikata. Misali Amerika duk duniyar mutum in dai ya yi laifi to za su hukunta shi daidai da laifinsa, amma a kasarmu ta Nijeriya babu doka, ya kamata gwamnati ta yi la’akari da dukkan jami’ai tun daga Dan sanda har Hukumomi da ministoci ka da fa wannan sakacin ya sa mutane su fara daukar doka a hanunsu. Kamar Ni misali na yi karatun boko sosai, amma fa idan ka taba min yarinya fa ba ma doka, zan manta da doka ne kawai, ni da kai na zan dauki doka a hannuna matukar za ka taba min yarinya da sunan zaka aikata fyade da ita ko ka aikata.

 

Mun gode.

 

Dakta: Nima Nagode.

Previous Post

Ranar 5 Ga Agusta Masu Rubuta Jarabawar WAEC Za Su Koma Makaranta A Nijeriya

Next Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 14 A Jihar Kogi -‘Yan Sanda

Next Post

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 14 A Jihar Kogi -'Yan Sanda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
Arabic Arabic English English French French Hausa Hausa
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2323 shares
    Share 929 Tweet 581
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1486 shares
    Share 594 Tweet 372
  • CBN Ya Sake Fitar Da Sabbin Bayani Kan Dawo Da Tsofaffin Takardun Kudin Naira

    1395 shares
    Share 558 Tweet 349
  • Rikicin Takara Gwamnan Adamawa A APC: Kotu Ta Tsayar Da Hukunci Kan Nuhu Ribadu Da Yake Yiwa Binani

    1049 shares
    Share 420 Tweet 262
  • Yan sanda a Katsina sun cafke yaro dan shekara 13 saboda ya kashe yan ta’adda

    990 shares
    Share 396 Tweet 248
Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani

Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani

February 5, 2023
Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole

Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole

February 5, 2023
Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

February 5, 2023
Fashin Bakin Mako: Layuka Basu ƙare Ba Yayin Da Najeriya Ba Ta Da Kuɗi A Watan Zaɓe

Fashin Bakin Mako: Layuka Basu ƙare Ba Yayin Da Najeriya Ba Ta Da Kuɗi A Watan Zaɓe

February 5, 2023
2023: Peter Obi Ya Mayarwa El-Rufai Zazzafan Martani Kan Kalaman Kiransa Da Jarumin Nollywood

2023: Peter Obi Ya Mayarwa El-Rufai Zazzafan Martani Kan Kalaman Kiransa Da Jarumin Nollywood

February 5, 2023
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Hukumar NPC Kan Kidayar Da Aka Shirya

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Hukumar NPC Kan Kidayar Da Aka Shirya

February 5, 2023
Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani
Labarai

Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani

February 5, 2023
Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole
Labarai

Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole

February 5, 2023
Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC
Labarai

Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

February 5, 2023
Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani

Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani

February 5, 2023
Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole

Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole

February 5, 2023
Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

February 5, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani
  • Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole
  • Nafi Girman Nayi Karya – Sanatan Jam’iyyar APC

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2022 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In