Domin tsaro:- Hukumar FCTA ta rusa gini 400 da ba kan tsari ba, a Abuja
A ranar Lanadinnan ne Hukumar FCTA ta sanar da ruguza gidaje da gine-gine da bakan tsari suke ba guda 400 a babban titin Nnamdi Azikwe a garin Abuja.
Ikharo Attah, Shugaban hukumar wanda ya jogoranci rushewar gine-ginen yace anyi hakane domin tsaro da kuma kare Lafiya Al’umma.
KARANTA:-Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun farmaki wani yanki a Kudancin Kaduna
NAN, sun ruwaito cewar an saka jami’an tsaro da dama lokacin da ake ruguza gidajen domin bin doka, lamarin dai ya shafi Lugbe-Across, Lugbe-Beger, Car wash da Lugbe zone 5, in da aikin ya share sama da awa takwas a nayi.
Jami’an tsaron sun hada da Yan sanda, Sojoji, Jami’an Civil Defense, Jami’an Immigration da sauran hukumomin dake cikin Abuja.
Attah yace “hukumar FCTA ta sha karbar korafe-korafen Al’umma kan gine-ginen da bakan tsari suke ba”.
” A wancan satin munzo nan bayan rushe wasu gine-ginen amma mutane suka sake ginawa, Kuma mun kara rusa wasu gidajen da dama.”
Hukumar FCTA da sauran jami’an tsaro sun ce ba za su kame hannu suna hanin bata gari suna cin karansu ba babbaka ba.