Yan majalisun sunyi wannan Kiran saboda ganin Makarantun Islamiyyoyin sunfi gidajen kallon kwallon muhimmanci. Kamar yadda Jaridar premium ta wallafa
Yan majalisun Jahar Katsina sun kudiri niyyar maida gidajen kallon kwallon dake kananan hukumomin 34 dake Jahar zuwa Islamiyyoyi.
Yan majalisun sun fara hakane bayan Dan majalisa mai wakiltar Jibia Mustapha Yusuf Jibia ya gabatar.
Yusuf yace, idan kudirin ya karbu zai taimaka akan rashin tsaron da jahar ke fama dashi.
KARANTA:- Shugaban Kasa ba dole sai ya fito daga Kudu ba: Inji Zulum
Har ya bada misali, inda yake cewa lokacin da akai sulhu da Yan bindiga sun bada korafin rashin Makarantun Islamiyyoyin da zasu sanya yaransu. Idan akai hakan zai basu damar inda zasu sanya yaransu.
Haka kuma idan aka tabbatar da kudirin zai rage yawan yara dake yawo kan Unguwanni suna bara.
Yusuf Jibia yace yawancin gidajen kallon kwallon ambarshi inda Yan iskan gari da miyagun mutane ke zaunawa.
A wani labarin:- Dubu 50 aka bani inkai buhu 173 na Wiwi Daura
An cafke wani da ake kira Mista Sunday Isaac, Mai kimanin shekaru hamsin, tare da buhu 173 na Wiwi ya dauko daga Zariya zuwa Daura,
Yace an yimashi alkawrin dubu hamsin idan yakai su lafiya Ya bayyana hakane Lokacin da Hukumar NCDSC suke tuhumarsa
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar an cafke Sunday Isaac tare da Hamisu Salisu yaron Motar, in da marukin motar ya ar ce.
Mai magana da yawun jami’an NCDSC Mohammed Tukur, ya bayyana haka lokacin da yake mika wadanda aka kama ga hukumar NDLEA.
Kamar yadda yace sun sami labarin shigowa da kayan nan take suka bazama don cafke su. Yace sun sami sa’ar kamasu ne da misalin karfe 7:30 a ranar 6, July 2021.
Kayan dai anyo dakon sune tun daga Legas a babbar mota tare da lodin kifi, wanda za’a kawoma wani babban dillalin kifi dake Katsina
Comments 1