Tsohon shugaban kasar Ghana, John Mahama ya roki gwamnatin Nijeriya da ta bude boda harkokin kasuwanci su ci gaba a yankin Afirka ta kudu.
Mahama ya yi rokon ne a lokcin da yake jawabin a wajen wani taron bunkasa tattalin arziki a kasashen Afirka a Legas.
Ya ce rufe bodar da Nijeriya ta yi ya jawo wa ‘yan kasuwan Ghana, Togo da Cote D’Ivoire koma baya.
“Ina da tabbacin ‘yan kasuwan Nijeriya da suka dogara da wadannan kasashe su ma suna shan wahala sakamakon rufe kan iyakokin nan. Bayan sa hannu a cikin yarjejeniyar nan tsakanin Nijeriya da makwabtanta, zan yi amfani da wannan damar wajen rokar gwamnatin Nijeriya da ta bude bodojinta don harkokin kasuwanci su ci gaba da gudana,” inji shi.