Tsohon shugaban kasa Amurka, Donald Trump ya shigar da gidan Talabijin na CNN kara a gaban kotun kasar, yana mai zargin kafar yada labaran da bata masa suna.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Trump a karar da ya shigar, ya bukaci kotu ta tursasawa kafar yada labaran ta CNN ta biya shi kudi, Dala miliyan 475, sakamakon abinda ya kira bata suna da cin kashi da aka yi masa.
KARANTA ANAN: Sanata Uba Sani Ya Yaba Da Wani Taron Horaswa Ga Malaman Addinin Musulunci
Cikin kunshin karar da Trump ya shigar a wata kotu dake birnin Florida na kasar Amurkan, ya ce CNN tayi amfani da munanan kalamai akansa, tare da bayyana shi a matsayin matsoraci mai gudun shan kayi, wanda hakan ya sanya ba zai sake tsayawa takara a shekarar 2024 mai zuwa ba.
Lauyan Trump cikin kunshin takardun karar mai shafukan 29, ya ce gidan talabijin din ya kuma bayar da wasu bayanai na karya da cewa sune silar faduwarsa a zaben baya da aka gabatar, wanda Joe Biden yayi nasara akansa.
Sun kuma bayyana Trump a matsayin mai nuna wariyar launin fata, lokacin da yake mulkin kasar, wanda shima na daga cikin dalilan da suka sanya zaben ya bashi mamaki.
Donald Trump dai ya shiga takun saƙa da wasu kafofin yada labarai, irin su CNN, da New York Times, tare da cewa labaran karya suke wallafawa, ya kuma yi amfani da shafukan sada zumuntarsa wajen adawa da su.
A wani labarin kuma: An kama masu haƙar Ma’adinai 12 ba bisa ka’ida ba a Ogun
Jami’an hukumar tsaro ta So-Safe Corps mallakin jihar Ogun sun kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba 12 a yankin Ogun ta Gabas.