Sashen da ke lura da man fetur wato DPR a takaice, daga watan Janairun shekararnan zuwa yau ya kulle gidajen man fetur 40 a jihar Nasarawa sakamakon aikata laifuka daban-daban.
Alhaji Abdulrahaman Muhammad-Bima, Kunturola na DPR din a Lafia shi ne ya bayyanawa manrma labarai hakan a garin Lafiya a ranar Litinin.
Ya tabbatar da cewa daga cikin laifukan da suka aikata sun hada da; karkatar da man fetur din, rashin samar da yadda ake bukata, da kuma rashin ba da kariya da sauran su.
Ya kara da cewa gidajen man fetur din ya shafi kananan hukumomi 13 jihar wanda gidajen man fetur din na manya da kananan ‘yan kasuwa ne. Ya ce gidajen man fetur din an ci su tara sannan kuma aka rufe su. Ya ce an ci su tarar ne sakamakon karya ka’idojin DPR din.