Sashen Kula da Albarkatun Man Fetur na kasa, DPR ya yi gargaɗin amfani da wayar salula a gidajen mai.
Olusegun Daboh, mai kula da ayyuka na DPR a Jihar Osun shi ne ya bayyana hakan, inda ya ce yin hakan abu ne mai haɗari wanda kai ya haddasa gobara.
Har wa yau, Daboh ya nemi masu ababen hawan da su riƙa kashe abin hawansu kafin a fara zuba musu man.
Sannan ya sake gargarɗin cewa; gidajen man da lasisinsu ya ƙare da kuma waɗanda suke sayar da man fiye da farashin da aka ƙayyade, inda ya ce za a hukunta su.