An kama Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Cango kan kisan fararen hula biyu a wani wuri dake kan iyakar kasar a jiya Lahadi. Kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya ya sanar
Rahotanni sun kuma bayyana cewa, wasu mutum 15 sun jikkata yayin da dakarun wanzar da zaman lafiyan suka kutsa kai cikin jama’a a hanyarsu dake iyakar kasar da Uganda.
Mista Muyaya ya ce gwamnati da tawagar jami’an wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, na gudanar da bincike kan lamarin.
Ya kara da cewa gwamnati na kira ga al’ummar Congo da su kwantar da hankulansu musamman wadanda ke yankin Kasindi da kuma daukacin lardin Kivu dake Arewacin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kusan Shekara Guda Likitoci A Abia Suna Yajin Aiki — NARD
A wani labarin kuma na daban.
Barazanar Kai Hare-Hare: An Tsaurara Matakan Tsaro A Jihar Legas
Biyo bayan barazanar da wasu kungiyoyin ta’addaci suka yi na kaiwa wasu manyan biranen Najeriya hare-hare a jiya, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bayyana cewa ta tsaurara matakan tsaro a kusa da wuraren da ake gudanar da ibada da wuraren shakatawa a fadin jihar.
Dangane da barazanar harin ta’addancin da aka shirya kaiwa manyan biranen kasar nan da suka hada da Legas da Kuma babban birnin tarayya Abuja Wanda ya karade shafukan sada zumunta na zamani.
Idan za a iya tunawa, a cikin makon da ya gabata, ‘yan ta’adda sun kai hare-hare da dama a wasu unguwannin dake cikin birnin tarayya Abuja, inda suka yi ta kashewa tare da yin awon gaba da wasu da dama a lokacin faruwar farmakin.
Sai dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Legas, Abiodun Alabi, ya ce an sanya hukumar leken asiri ta jihar (SIB) da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Alabi, ya Kara da cewa rundunar na aiki tare da sauran jami’an tsaro domin samar da tsaro a fadin jihar, tare da ba mazaunan Legas tabbacin yin sana’arsu ta yau da kullun ba tare da wata fargaba ba.
A karshe ya umurci mazauna jihar Legas da su kasance cikin taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani motsi akan duk wasu mutane da suke zargi ga hukumomin tsaro ba tare da bata lokaci ba.