Rahotanni sun bayyana cewar tawagar tsofaffin Yan wasan Chelsea ne zasu yi dirar miki zuwa dora kungiyar bisa turbar daukar kofuka.
A cikin wannan makon jagororin kungiyar Chelsea suka damka ragamar jagorancin Kungiyar Chelsea a hannun Frank Lampard, matsayin Kociya mai cikakken Iko.
A lokacin da aka bayyana Lampard din a matsayin sabon mai bayar da horo, tsofaffin Yan wasan Chelsea Drogba da Makelele zasu yi ma Lampard rakiya.
Drogba, ya kasance manyan Yan wasan Chelsea da suka kafa tarihi, Dan wasan ya zurawa Chelsea kwallaye 164 a cikin wasanni 381, daya bugawa kungiyar.
Haka shima Makelele, ya bugawa kungiyar wasanni 217, kuma shima ya taka rawar gani.