Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana cewa akwai wasu bata gari dake shirin tayar da zaune tsaye, a lokacin bukukuwan mika mulki da za a yi a wasu jihohin kasar nan ranar 29 ga watan mayu.
A sanarwar da kakakin Hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar, hukumar ta bukaci jama’a da ƴan jarida da ƴan kungiyoyin farar hula da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar da su bi ka’idojin da aka tsara a lokacin bikin a ko’ina a fadin kasar.
KU KARANTA: Gobara Ta Tashi A Gidan Da Ganduje Zai Koma Bayan Rantsuwa
A wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, hukumar DSS ta ce mutanen suna son yi wa aikin jami’an tsaro kafar Ungulu, tare kuma da tayar da hankalin jama’a domin jefa tsoro ga ‘yan kasar a lokacin.
Haka kuma sanarwar ta shawarci jama’a da su yi watsi da labaran karya ko na kanzon-kurege da na zuzuta al’amura da kuma duk wani abu na neman razanarwa.
Hukumar ta kuma shawarci duk wani mutum da ba shi da takardar izini ko ta tantancewa da ya kauce wa shiga wasu wuraren a lokacin da ake bikin.
Hukumar ta DSS ta bai wa jama’a tabbacin ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin bukukuwan sun wakana lami lafiya cikin nasara a ko’ina a fadin kasar.
A ranar Litinin 29 ga watan nan na Mayu 2023 ne za a yi bikin mika mulki da rantsar da sabon shugaban kasa a Abuja da kuma gwamnoni a wasu jihohin Najeriya.
A wani labarin kuma: Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Mika Bayanan Gwamnatinsa Ga Tinubu
A yayin da ya rage kwanaki 5 shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika takardun mika mulki ga zababben shugaban kasa Tinubu.
Wannan ya yi dai-dai da Dokar Zartaswa ta 14 wadda ta ba da umarnin.
Mika bayanan shine domin gabatar da tsarin manufofin gwamnati mai zuwa.