A gobe Litinin ake sa ran gurfanar da Omoyele Sowore gaban kotu, tsohon dan takarar shugabancin Nijeriya na jami’iyyar AAC, kuma jagoran zanga-zangar juyin juya hali ta ‘RevolutionNow.’
Sowore dake tsare a hannun hukumar tsaro ta DSS, na fuskantar tuhume-tuhumen da suka hada da cin amanar kasa, da kuma almundahanar kudade.
Kwanaki shida da suka gabata kotu ta bada umarnin sakin Sowore bayan cika ka’idojin Beli a ranar 25 ga Satumban da muke, amma hukumar DSS ke ci gaba da tsare shi, saboda sabbin tuhume-tuhumen data bijiro da su akansa.
A watan Agustan da ya gabata, babbar kotun Nijeriya ta bada izinin tsare jagoran zanga-zangar ta RevolutionNow amma tsawon kwanaki 45.