Dubu 50 aka bani inkai buhu 173 na Wiwi Daura
An cafke wani da ake kira Mista Sunday Isaac, Mai kimanin shekaru hamsin, tare da buhu 173 na Wiwi ya dauko daga Zariya zuwa Daura,
Yace an yimashi alkawrin dubu hamsin idan yakai su lafiya.
KARANTA:- An rufe Makarantun Firamare a Abuja saboda rashin albashi
Ya bayyana hakane Lokacin da Hukumar NCDSC suke tuhumarsa.
Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewar an cafke Sunday Isaac tare da Hamisu Salisu yaron Motar, in da marukin motar ya ar ce.
Mai magana da yawun jami’an NCDSC Mohammed Tukur, ya bayyana haka lokacin da yake mika wadanda aka kama ga hukumar NDLEA.
Kamar yadda yace sun sami labarin shigowa da kayan nan take suka bazama don cafke su. Yace sun sami sa’ar kamasu ne da misalin karfe 7:30 a ranar 6, July 2021.
Kayan dai anyo dakon sune tun daga Legas a babbar mota tare da lodin kifi, wanda za’a kawoma wani babban dillalin kifi dake Katsina.
Comments 2