Lamarin Samun haihuwa ko ta halin Kaka a Najeriya na ci gaba da zama ruwan dare, wannan ne wata kila ya sa mata da yawa suka zaɓi zama iyaye ba tare da sun shirya ba.
Wani matashi mai suna @MrAlan a shafin Tuwita ya fito ƙarara ya bayyana maitar shi ta neman haihuwa ido rufe.
Matashin ya ce a halin da ake ciki yana bukatar samun budurwa yar shekara 20 zuwa 25 da zai mata ciki ya bata dubu hamsin don ta haifa mishi jariri.
“Ina bukatar matashiya yar shekara 20 zuwa 25 da zan mata ciki, zan biya ta dubu hamsin” Kamar yadda ya wallafa a shafin nasa.
To sai dai bisa ga Dukkan alamu wannan al’amari bai yiwa mabiyan shi daɗi, domin an ce idan ka san na faɗa to lallai ba ka san Na mayarwa ba.
Wannan yasa mabiyan shi da dama suka yi ta furta kalaman Allah wadai da nuna fushin su, yayin da wasu kuma suka daina bin shi kwata-kwata.
Kawo yanzu dai matashin bai bayyana dalilin shi na yin wannan aiki ba, to amma matsalar yin kuɗi ido rufe ga matasan mu na ci gaba da ta’azzara ta inda wasu bikaye ke sanya su ala tilas sai sun zi da jariri ko abu mai kama da haka.