Rundunar soji karkashin atisayen ‘Safe Haven’ a ranar Juma’a ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka addabi karamar hukumar Zangon Kataf, a jihar Kaduna.
An cafke wadanda ake zargin ne biyo bayan wani bayanin sirri da aka samu a kansu, kuma a halin yanzu suna karkashin ikon rundunar sojin, inda suke gudanar da bincike kansu a matakin farko.
A cewar kwamishinan bayanan sirrin tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, “Dakarun soji karkashin atisayen ‘Safe Haven’ tare da hadin guiwa da dakarun shelkwatar tsaro ta kasa sun cafke wasu ‘yan bindiga biyu a tsakanin garin Ungwan Wakili da Zango kauye, a karamar hukumar Zango Kataf.
KARANTA WANNAN: Yadda Cutar Korona Ta Kama Mahaifiyata A Kurkuku -Muhammad Zakzaky
“Mutane biyun da ake zarginsu, Abdulhameed Abubakar Bala da Abubakar Abdulhameed Garba, an cafke su ne biyo bayan samun bayanan sirri, a zarginsu da kai hare hare a Gora Gan, Damkasuwa, Zonzon da Kwaku a cikin watan Disambar 2020.
“Wadanda ake zargin suna hannun rundunar soji inda ake gudanar da bincike a kansu a matakin farko.
“Gwamna Nasir El-Rufai ya samu wannan rahoto, kuma ya nuna jin dadinsa, ya kuma jinjinawa dakarun sojin bisa namijin kokarinsu na cafke ‘yan ta’addar. Ya bukace su da su tabbatar da sun gudanar da bincike a kansu.”