Rundunar ‘yan sandan birnin Dhaka a kasar Bangladesh ta cafke wasu ‘yan Najeriya 11 bisa zarginsu da hannu a wata badakalar damfarar ta kafar sada zumunta na Facebook, kamar yadda wata jarida a Bangladesh ta intanet, bdnews24 ta ruwaito.
An kama ‘yan Najeriyar ne tare da wani dan kasar Bangladesh bisa zargin karbar kudi daga hannun mutane bisa karyar musayar kudin kasar na Taka zuwa dalar Amurka.
Rundunar ‘yan sandan, a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Alhamis, ta ce an kama wadanda ake zargin ne a wani samame daban-daban da takai a Dhaka, babban birnin kasar, ranar Laraba.
Wadanda ake zargin ‘yan Najeriyar sun hada da Henri Osita Okechukwu, Chisom Emmanuel Obiajulu, Okeke Peter, Obinna Sunday, Oneka Amba, Chisom Anthonoy Ekwenze, Okeyea Azubike, Anuyarah Ojuyemena Daniel, Anuruka Jinika Francis, Luke da Domado Chinedo.
Rahotanni sun bayyana cewa wata ‘yar kasar Bangladesh mai suna Chadni Akter da ta boye sunan ta tare da yin badda kama da ma’aikaciyar kwastam.
An jiyo wani karin kwamishina a sashin bincike na DMP AKM Hafiz Akter yana cewa, “Shugabannin kungiyar damfarar su ne Osita Okechukwu da Chisom Emmanuel. Kuma Sun kasance suna ci gaba da wannan aiki tare da abokan aikinsu na Bangladesh ta hanyar rarraba kudaden da aka wawure ga sauran mambobin kungiyar.
“Sauran mambobin kungiyar sun yi zambaci mutane makudan kudade tare da alkawuran kyaututtuka masu tsada da kuma saka hannun jari bayan kulla abota ta sirri da wani hafin Facebook na bogi a matsayin Ba’amurke ko Bature.”
Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da injin buga Dala na Bogi dala, wayoyi 17, kwamfutar tafi-da-gidanka guda biyu, kwalabe masu guba da dai sauran su.
A cewar Aktar, wasu ‘yan kasar Bangladesh, baya ga Chadni, suma suna da hannu a cikin kungiyar, ya kara da cewa za’a dauki matakin shari’a a kan wadanda ake zargin.