Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu motocin bas guda biyu na ‘yan kasuwa da ke dauke da manyan katun din alburusai masu kisa.
Daily Post ta ruwaito cewa, Haka kuma an gano wasu babura guda uku da aka kankwance su daban-daban.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Matashin Da Ake Zargin Sha Muggan Kwayoyi, Sun Kama Abokansa
Jami’an ‘yan sanda sun kama mutane uku da ake zargi a Estate Poromope, kan titin Ijede a Ikorodu.
Wadanda aka kaman su ne: Tukur Abdullah mai shekaru 35 da Muazu Telim mai shekaru 50 da Dahiru Idris mai shekaru 36 kamar yadda jami’in hulda da jama’a Benjamin Hundeyin ya sanar.
Kakakin ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen uku na kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina ne daga jihar ta Legas.
An kama kayayyakin tare da baje kolin mutanen da kuma motocin masu lamba KMC 438 YK da KMC 394 XF.
Kakakin ya kuma ce, An mika lamarin zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Legas da ke Ikeja domin ci gaba da bincike.
A WANI LABARIN KUMA: Atiku Ya Fi Cancanta Ya Zama Zabin Yan Najeriya a 2023, Saraki
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi shiru kan rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Saraki wanda ya rufe baki tun bayan rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a ranar 28 ga watan Mayu ya kada shi, a ranar Asabar, ya bayyana cewa ya tafi hutu.