Jami’an hukumar EFCC sun bayyana cewa su na binciken wani mutum da ake zargin ɗan damfara ne, bayan kama shi da aka yi da tarin katin cirar kuɗi ATM har guda 2,886.
An kama mutumin a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, a lokacin da ya ke ƙoƙarin hawa jirgi zuwa daular Larabawa, wato Dubai.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar na EFCC, Dele Oyewale ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, ya ce wanda ake zargin mai suna Ishaq Abubakar, jami’an Kwastan na Najeriya ne suka damƙe shi a filin jirgin na jihar Legas.
Bayan sun kama shi ne suka damƙa shi a hannun hukumar EFCC reshen jihar Legas, domin ci gaba da bincike a kansa.
EFCC ta ruwaito mataimakin Kwanturola na Kwastan Abdulmumini Bako ya ce, wanda ake zargin daga Kano ya isa filin jirgin, a kan hanyar sa ta hawa jirgi daga Legas zuwa Dubai.
Ya ce wanda ake zargin ya yi niyyar fita zuwa Dubai ne ta jirgin Emirate, an gan shi tare da wani hadimin da ya riƙa kai da kawo a filin jirgin domin ganin cewa mutumin ya samu tsallakewa ya hau jirgi.
” Mutumin ya ɓoye katin ATM ɗin a cikin kwalayen Taliyar yara.
Wannan ne ya sa aka tilasta cewa sai an yi masa binciken-kwakwaf.”
Jami’in EFCC da ya karɓi wanda ake zargin, ya ce za a yi bincike, kuma ya tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka kama ya na da hannu a cikin wannan harƙallar.
Jami’in ya ƙara da cewa ana zargin harƙalla ce ta karkatar da kuɗaɗe tsakanin wasu mutane da kuma ma’aikatan banki.
Ya ƙara da cewa sun lura kwanan nan ana yawan buɗe asusun ajiya a banki barkatai, ba tare da bankuna na tantance waɗanda suka buɗe asusun an san su ido-da-ido ba.