Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar babura, da ya mai suna Aliyu A. da Mohammed Dani a garin Minna babban birnin jihar Neja.
Jami’an Ofishin rundunar Yan sanda dake GRA ne kama wadanda ake zargin a Minna, a lokacin da suke gudanar da aikinsu da misalin karfe 2:30 na ranar Lahadi, yayin da wadanda ake zargin suka yi yunkurin kashe daya daga cikin wadanda su kazo satar musu mashin .
An bayyana cewa wadanda ake zargin sun hau babur guda daya wanda aka fi sani da okada daga unguwar Fadukpe da ke Minna zuwa yankin Shanu, inda suka dirkawa Dan Acaban mai suna Mohammed Idris Sakewa Guduma a kai, sannan suka dauki babur din shi.
Shaidu sun ce ihun wanda abin ya shafa ya jawo hankalin jama’an dake kusa da wajen, inda nan take suka bi sawun barayin, kuma suka kama su batare da Bata lokaci ba, Kana suka mika su ga rundunar ‘yan banga na Fadikpe wadanda su kuma suka kai su wajen Ofishin ‘yan sanda, yayin da aka garzaya da wanda lamarin ya rutsa da shi, zuwa asibitin ‘yan sanda, dake Unguwan-Daji, na garin Minna.