Gwamnan Jahar Niger Abubakar Sani Bello, ya gargaɗi ƙauyuka a jahar dasu daina ɓoye ƴan ta’adda.
Gwamnan ya bada gargaɗin ne a Minna a ranar Laraba, inda yace wasu al’ummomi na ɓoye ƴan ta’adda domin su kare kansu.
Yayi gargadin cewa “nan bada jimawa ba zamu bayyana waɗannan ƙauyukan a matsayin ƴan ta’adda. Idan kana ɓoye ƴan ta’adda, to kaima shine. Koda baka ɗauki bindiga ba, kana ɗaya daga cikin su. Domin kana jefa rayuwar jami’an tsaro cikin haɗari, da kuma al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Wani Mutum ya Bankawa Jirgin Kasa Wuta a Kwara
“Wannan yaƙin bawai na jami’an tsaro bane, namu ne, domin kowa najin tsoro akan abinda ke faruwa.
“Abun baƙin ciki wasu al’ummomi a ƙauyuka domin kare kansu daga waɗannan ƴan ta’adda, suna ɓoye ƴan ta’adda.
Ya shawarci al’umma musamman waɗanda ke ƙauyuka dasu zama masu kula da maƙwabtansu da waɗanda ke kusa dasu.
Gwamnan ya bayyana cewar” idan kaga tattalin arzikin mutum ya canja a dare ɗaya, da yadda yake kashe su, to ya zama abun zargi. Kuma dole zaka kai rahoton wannan mutumen ga jami’an tsaro, idan baka da hujjoji ka sanar da jami’an tsaron.
Bello ya bayyana damuwa na yadda wasu makiyaya suka zama ƴan ta’adda bayan sun rasa abun na kansu ga ƴan ta’adda.