Rahoton cibiyar IQ Airvisual mai muhalli a kasar Switzerland ta fitar da wani rahoto akan gurbacewar yanayi a duniya, inda ta sanya Nijeriya a matsayin kasa ta 10 a mafi gurbacewar yanayi a duniya.
A cikin rahoton har wala yau ya bayyana birnin Kano a matsayin mafi gurbacewar iska a fadin nahiyar Afirka, inda gurbacewar iskar ta kai kashi 53.4 cikin dari.
Dangane da dalilan da suka haddasa gurbacewar iskar, rahoton ya zayyano wasu abubuwa kamar haka;
- Amfani da itace da kananziri da gawayi yayin girki
- Dagwalo da sharar gona
- Hayakin ababan hawa
Rahoton ya kuma nuna cewa birnin Kampala ne ke biye wa na Kano a gurbacewar iskar, inda birnin Fatakwal na Nijeriya ya zama na uku sannan birnin Adis Ababa ya zamo na hudu a jadawalin gurbatacciyar iskar.
Rahoton ya ce gurbatacciyar iska da ke Nijeriya ta kai kashi 44.8 cikin 100, inda Uganda da Habasha suke biye mata baya.
Rahoton na cibiyar IQ Airvisual ya ce nahiyar Afirka na fama da gagarumin rashin hanyar tattara bayanan bibiyar iska mai inganci, yayin da kuma take fuskantar kalubalan gurbacewar iska masu alaka da ita kanta nahiyar.
Bbc Hausa sun labarto rahoton na cewa; Afirka na da bunkasar Birane mafi sauri ga kuma karuwar jama’a da ke kwarara zuwa manyan birane, inda gurbatacciyar iska ta fi yawa.
Kuma manyan kafofin gurbatacciyar iska sun hadar da amfani da makamashi irin su gawayi da Itace da kalanzir wajen girki, lamarin da ya sa matsalar ta zama gagara badau a yankunan karkara saboda takaitattun kayan more rayuwa da hanyoyin samun makamashi mai tsafta.
Masana sun ce gurbatacciyar iska ce sanadi na hudu a duniya mafi tasiri wajen haddasa mutuwar fu-ju’a.
Rahoton ya ce kasar Bangaladesh ce ta fi rashin iska mai inganci a tsakanin kasashen duniya, inda take da gurbatacciyar iska kashi 97.1, sai k’asar Pakistan, Indiya kuma na biye musu da gurbatacciyar iska kashi 72.5.
Rahoton ya ce Nijeriya, ita ce kasa ta goma a duniya kuma mafi gurbatar yanayi a fadin nahiyar Afirka, inda take da gurbatacciyar iska har kashi 44.8 cikin 100. Sai Uganda a matsayi na biyu, Habasha, matsayi na uku.
Binciken na cibiyar IQ Airvisual ya ce gurbatacciyar iska, gagarumar kasadar muhalli ce ga lafiyar mutane a yau, inda kiyasi ya ce matsalar na janyo mutuwar bakwaini miliyan 7 duk shekara a duniya.