Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ya mallaki kwarewar da ake bukata wajen gudanar da mulkin jihar Kano.
Yayin da ya bayyana a wani shirin siyasa na “Political Update” a gidan talbijin na Najeriya NTA, ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda ya yi aiki a gwamnatoci uku a matsayin shugaban karamar hukumar wa’adi biyu, tsohon kwamishinan noma har sau uku kuma a halin yanzu mataimakin gwamnan jihar ne, hakan ya nuna kwarewar sa sama da ta sauran yan takarar dake zawarcin kujerar.
KARANTA ANAN: Shugaban Kasa: Dalilin Da Ya Sa Peter Obi Ya Fi Atiku, Da Tinubu – Shugaban Yarabawa
“Mutanen Kano sune zasu iya yanke hukunci saboda sun san wane dan takara ne ke da gaskiya da kuma karfin shugabancin su, tare da goyon bayansu, don haka za mu ci zabe”.
“Gwamnatinmu mai ci ta yi ayyuka da dama kuma a bayyane suke, baya ga haka abin yabawa a wajen alumma sakamakon kokarinta na ci gaban jihar.”
Gawuna ya ci gaba da cewa rarrabuwar kawuna a sauran jam’iyyun siyasa wata fa’ida ce a gare su, ”mu jam’iyyar APC muna nan daram kuma mun a hade yake.
“Wadanda suka shigo cikin jam’iyyar mu mutane ne da suka yi imani da akida da ka’idojin jam’iyyar APC domin mun zabo ’yan takara masu inganci.
Za su ba da gudunmawa sosai don ganin mun samu nasara a lokacin zabe amma wadanda suka sauya sheka daga gare mu suna yin su ne saboda burin su tsaya takara bayan rashin nasarar da suka yi a zaben fidda gwani na jam’iyyar,” inji Gawuna.
A wani labarin kuma: Kwankwaso Yayi Alkawarin Magance Matsalar Tsaron Najeriya Idan Har…
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar idan aka zabe shi shugaban Najeriya a 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin Keffi, Dakta Shehu Chindo Yamusa III ziyara a fadarsa da ke karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.