Kungiyar likitocin Nijeriya reshen Legas ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani, bayan da a jiya Laraba ta baiwa ‘ya’yanta umurnin daukar matakin ta hanyar zama a gida.
Sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar likitocin ta kasa reshen Legas, Dakta Moronkola Ramon, ta ce shiga yajin aikin ya zama tilas duba da yadda jami’an tsaro suke cin zarafin Likitocin dake kokarin isa wuraren aiki da kuma komawa gidajensu a daidai lokacin da dokar hana zirga-zirga ta soma aiki daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a jihar ta Legas.
Tun farko dai a yayin sanar da kafa dokar hana zirga-zirga don yakar annobar Korona da kuma lokacin sanar da sassauta dokar, shugaban kasa Buhari ya zayyana daidaikun mutane ko ma’aikatan da dokar hana fitar ba ta shafa ba, cikinsu harda Likitoci.
Rfi sun ce baya ga likitoci da sauran jami’an lafiya, bangarorin da dokar hana fitar bata shafa ba sun hada da ‘yan jarida, ma’aikatan gona, fannin man fetur da sauran masu ayyukan da al’umma ke cikin bukatarsu.