Mataimakin shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, yace Nigeria zata cigaba da kasancewa ƙasa ɗaya, duk da irin matsalolin da take fuskanta a halin yanzu.
Mataimakin shugaban Ƙasar ya ƙara dacewa duk da irin matsalolin tsaro, da tattalin arziki, da addini, da ƙabilanci, amma Nigeria zata cigaba da kasancewa ƙasa mai haɗin kai, mai zaman lafiya.
Ya bayyana haka a taron murnar samun ƴan cin kai kashi na 61 na Kungiyar Kiristoci ta Nigeria, a wata cibiya dake Abuja, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Ɗalibin jami’ar Imo, da sukayi garkuwa da shi
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ƴan Majalisa, da Alƙalai gami da ɓangaren majalisar zartarwa ta ƙasa.
Akwai kuma shugaban cocin Redeemed Christian Pasto Enoch Adeboye, da shugaban ƙungiyar kiristoci ta Nigeria Reverant Supo Ayokunle da sauran su.
Osinbajo yace yanzu ƙasar Nigeria itace tafi kowacce yawan masu ilmi, kuma wadda tafi kowacce yawan waɗanda suka fi yawan masu sana’o’i a Afrika.
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa, a halin yanzu jahohi 10 cikin jahohi 36 sun fi wasu ƙasashe 15 ƙarfin tattalin arziki na Afrika.
“Muna da sanannun mutane maza da mata da suka yi fice a ɓangaren kimiyya da fasaha, da wasan ƙwallo da kasuwanci da sauran su.
“Matsalolin dake faruwa a halin yanzu baza su sanya mu dawo baya ba, domin zai wuce ya zamanto tarihi.