Duk da matsin tattalin arziƙi da ake fama da shi sakamakon cutar Korona, kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki sun ƙara kuɗin wutar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin da aka ɗiba na jinkirta yin ƙarin yake cika a yau Talata.
Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa aƙalla kamfanoni uku sun ƙara farashin kamar yadda Hukumar Kula da Hasken Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta amince.
A baya dai NERC ta ce dole kamfanonin su nemi amincewar abokan hulɗarsu kafin yin ƙarin tare kuma da cewa ƙarin ba zai shafi wadanda ba su samun wutar ta aƙalla sa’a 14 a rana ba.
Kamfanin raba wutar lantarki na Kaduna (K-power) ya tabbatar da yin ƙarin farashin a wata sanarwa da ya fitar.
https://dimokuradiyya.com.ng/wutar-lantarki-ƙarin-kuɗin-wutar-lantarki-ba-kowa-zai-shafa-ba-nerc/
A cewar kamfanin, “Daga ranar Talata, 1 ga watan Satumbar 2020, sabon ƙarin kuɗin wuta zai fara aiki.
“Abokan hulɗarmu da ke rukunin D da E, ƙarin bai shafe su ba, amma na rukunin A kuwa farashin ya tashi daga N40 a kan kowane Kilowatt da suke biya a baya zuwa N56.31.
“Wannan ƙarin ya shafi watannin Satumba zuwa Disambar 2020 ne kawai,” inji sanarwar.
Shi ma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na shiyyar Legas da ke Ikeja ya tabbatar da ƙarin, ko da yake ya ce kawo yanzu bai shafi abokan hulɗarsu da ke samun wuta ƙasa da sa’a 12 ba, har sai zuwa lokacin da aka inganta ta.
A ranar Litinin ne kamfanoni ukun suka miƙa rahoton ci gaban samuwar wutar ga NERC, ta kuma amince musu da su yi ƙarin, yayin da ragowar ke jiran yin haka zuwa ƙarshen wannan watan.