Kasar Saudiyyah ta hana kamfanin beIN Sport, wacce ke da ikon tallata gasar Firimiyar Ingila a gabas ta tsakiya daga gabatar da shirye-shirye a kasar, wanda hakan na nufin kasar ba za ta kalli wasannin gasar Firimiyar Ingila ba, duk da shirin da take na kokarin sayen kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United.
Mahukuntan gasar na ta jiran amincewa da tayin fam miliyan 300 kudin sayen kungiyar ta Newcastle United da aka yi, sai dai wannan matakin da gwamnatin Saudiyya ta dauka zai iya dakatar da komai.