Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma sun kammala taron su na kwana guda a Mali ba tare da samun nasarar kulla wata yarjejeniyar kawo karshen rikicin siyasar kasar ba.
Shugabannin guda biyar da suka hada da na Nijar Mahamadou Issofou dake shugabancin ECOWAS da kuma takwarorinsa na Nijeriya da Ghana da Cote d’Ivoire da kuma Senegal sun gana da shugaba Ibrahim Boubacar Keita da kuma ‘yan adawa a karkashin shugabancin Imam Mahmoud Dicko dake neman ganin ya sauka daga mukaminsa.
Rahotanni sun ce kafin saukar shugabannin a Bamako an samu kwarya-kwaryar zanga-zanga kusa da tashar jiragen saman kasar daga masu neman ganin shugaban kasar ya bar mukaminsa.