A daidai lokacin da wa’adin mulkin gwamnoni masu barin gado ke karewa, hukumar EFCC ta fara bincikarsu. Ana zargin wasu daga cikin gwamnonin da laifukan cin hanci da rashawa.
Wani jami’in hukumar ta EFCC ya bayyana wa Manema Labarai cewa, gwamnonin ma su barin gado wadanda ke da kes da hukumar sun san kansu saboda haka ana shawartarsu da su kawo kansu wurin bincike bayan karewar wa’adin mulkin su.
Jami’in ya shaida mana cewar, hukumar ta dauki dukkan matakan da ya dace don ganin cewa gwamna ne, mataimaki ko ma wane ne bai gudu ya bar kasar ba bayan bayar da ragamar mulki.
Tuni dai, hukumar ta EFCC ta cafke wani mutum mai suna Murtala Muhammad wanda a ke zargin kani ne ga Farfesa Abdullahi Shinkafi, sakataren gwamnatin jihar Zamfara, wanda ta samu dauke da kudi naira miliyan 60, bayan rahoton zargin mutumin da a ka kai ma hukumar.
Shi dai mutumin, an cafke sa ne a wani gida mai lamba 145 da ke unguwar Igala a garin Gusau, babban birnin jihar.
Kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce sun kama shi ne a cikin wata mota kirar jip parado dauke da jakar bako shake da kudi ‘yan Naira dubu-dubu; kowace jaka na dauke da miliyan 15, wanda jimillar ya bada miliyan 60, sai kuma albarusai da bindigar fistul.
Mista Orilade ya ce, da zaran sun kammala binciken sa, za su gurfanar da shi a Kotu.