Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna ya ce zai ci gaba da korar ma’aikata, tare da rusa gidaje wadanda aka gina ba bisa ka’ida ba.
Gwamna El-Rufai ya ce zai ci gaba da aikin rushe rushen har zuwa karfe sha daya na daren ranar 29 ga watan Mayu.
KU KARANTA: Tinubu Ya Dawo Najeriya Kwanaki 8 Kafin Rantsar Da Shi
El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a wajen kaddamar da littafi a Kaduna ranar Asabar, inda Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya yaba da jajircewarsa na fadin gaskiya ga mulki.
El-Rufai ya ce zai ci gaba da korar duk wani bata gari da ya cancanci kora, a kokarin gwamnatinsa na tabbatar da komai na tafiya yadda ya kamata.
A sakon da ya aike wa taron, zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana gwamna El-rufai a matsayin mutum mai kwazo.
“Ba wa El-rufai duk wani aiki, zai yi,” in ji shi Gwamna Wike wanda shi ne babban bako mai jawabi a wajen taron, ya ce bai taba ganin dan Najeriya mara tsoro kuma mai fadin magana irin El-Rufai ba.
Gwamnan jihar Ribas ya ce mutanen da za su iya fadin gaskiya kan mulki a kasar nan ba abu ne mai sauki ba, kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-rufai ne kadai ke da hazaka da jajircewa wajen yin hakan, hatta a jam’iyya mai mulki da ya ke.
Ya ba da gudummawar Naira miliyan 20 don kaddamar da littafin, ya kuma shawarci sauran bakin da suka halarci bikin da su sayi littattafan a ajiye su a dakunan karatu na gwamnati da na makarantu masu zaman kansu a Nijeriya.
A wani labarin kuma: Ganduje Ya Biyawa Dalibai Kudin Jarrabawar NECO, NABTEB, NBAIS
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano ya yabawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, bisa amincewa Da sakin kudin jarrabawa ga daliban dake shirin gama makarantar sikandire.
Majalisar zartarwa ta gwamnatin Kano ta amince da biyan sama da Naira Biliyan ɗaya, domin dai biyawa dalibai su rubuta Jarrabawar NECO, NBAIS da NABTEB a shekarar 2023.