Tsohon Sanatan Kaduna a majalisar Dattijan Najeriya Sanata Shehu Sani ya caccaki yan Najeriya dale murnar Mutuwar Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu a jiya sakamakon hatsarin Jirgin sama.
Attahiru yana hanytsa ta zuwa Kaduna ne tare da wasu manyan Hafsoshin soji goma sa’ilin da jirgin nasu ya yi hatsari yayin sauko a babban filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa.
Yayin da yan Najeriya ke juyayin mutuwar Hafsan Sojin, Shehu Sani ya yi zargin cewar akwai wasu masu mugun nufi da mutuwar tasa ta yi musi daɗi inda ya ce dukkanin irin wadannan mutane shedanu ne.