Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari ya ce duk wani wanda yake da bayani akan shi ya wawure kudaden mutanen jihar Zamfara, to ya zo ya fallasa shi. Yari ya yi wannan barazanar ne a ranar Lahadi a gidansa dake Talatan Mafara a yayin shugabannin jam’iyyar APC na jihar suka kai masa ziyara.
“Gwamnan ya ce; ina mai kalubalantar duk wanda ya ce na maishe da kayayyakin gwamnati na wa ko na wurare kudi a ciki da wajen kasarnan a yayin da nake gwamna da ya zo ya fallasa ni.” In ji shi.
Ya ci gaba da cewa; a matsayin na gwamna shi ne ya kashe kudi, kuma abin da ya yi ke nan wajen ci gabantar da jihar domin amfanar al’ummar jihar baki daya.
Yari ya ce a matsayinsa na mai imani, ya yi imanin cewa duk abin da ya same shi, to daga Allah ne. Ya ce; wadanda suke ganin za su iya karya shi, to ba za su yi nasara ba.