Alhaji Tanko Yakasai, babban mai fada aji, yace gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC, ta yiwa tsohon shugaban majalisan dattijai Abubakar Bukola Saraki karin karfin guiwa ne a tsarin siyasar sa. Kamar yadda Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, Alhaji Tanko Yakasai, cewa wayi sun gayyace shi don ya sami rauni a kan kudirinsa na neman shugabancin kasar nan a shekarar 2023.
Yace gaskiya yaji ba dadi, saboda Abubakar Bukola Saraki tamkar Dan sa ne.
KARANTA:- Tabbas Allah zai tsare Abba Kyari, cewar Ordinary President Ahmad
Yake cewa ” Na karanta a kafar sadarwa hukumar yaki da cin hanci ta gayyaci dana kuma Dan aminina Dakta. Olusola Saraki, watau Abubakar Bukola Saraki a ranar Asabar data gabata.”
“Ni dai ba zan shiga tsakanin abunda hukumar yaki da cin hanci ta gindaya ba, Ina fatan dai tuhumar da hukumar EFCC keyima Abubakar Bukola Saraki bata shafi siyasarsa ba, ko wani abu da ya shafi siyasar 2023 ba.”
“Ina fatan wannan ba zai zama cin fuska a siyasar Abubakar Bukola Saraki ba, Ni dai bana cikin kowace jam’iyyar Siyasa a Nigeria, ni dai kawai ina da burin Kare hakkin kowane mutum ne daga kowace kabila ya fito.”
A wani labarin
Tabbas Allah zai tsare Abba Kyari, cewar Ordinary President Ahmad
Ahmad Isah wanda akafi sani da Ordinary President, mai gidan Rediyon Brekete Family dake Abuja, yace Abba Kyari jarumi ne kuma zakakurin Dan sanda, yayi ayyukan yabawa sosai a kasar nan.
A halin yanzu dai an dakatar da Abba Kyari bisa laifin da ake zarginsa dashi na karbar cin hanci daga Ramon Abbas.
Ramon Abbas wanda akafi sani da Hushpupi, ya kasance dai kasurgumin dan damfara ne da yayi kaurin suna a duniya, an dai ruwaito ya baiwa Abba Kyari cin hanci dala miliyan daya kan ya kama wani da ya ci amanarsa.
Ordinary President, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gidan Rediyonsa, yace Kasar America bata kyauta ba da dake tuhumar Abba Kyari.
Kamar yadda ya fada “Wannan yanayin da Abba Kyari ya shiga, wadansu daga cikin Yan sanda suna murna, wadansu kuma suna ta gulma.”
“Kunata murna kuna jindadi, to bari na gaya maku, ko kun ki, ko ku so, da yardar Allah Abba Kyari ba zai tozarta ba, ayyukan da yayi a kasar nan yafi karfin a tozartashi koda zargin da ake masa ya zama gaskiya.”
“Kasar America ba ta isa ta gaya mana yadda za muyi rayuwa ba, America ba Aljannah bace, da akwai Yan shaye-shaye a America, akwai mazunata, akwai masu garkuwa da mutane, akwai Yan ta’adda daban-daban, me America za ta nunama kasashen Africa in banda rashin shugabanci na gari.”
“Muna tare da Abba Kyari, Kuma In Shaa Allah, Allah zai tsare mana shi.”