Duk Satar Da Ku Ka Yi Yanzu Ba Ta Da Amfani — Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin Da Ke Sukar Buhari
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP), ya caccaki gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun sake fasalin kudin Naira.
Babban Bankin Najeriya (CBN) wanda ya gabatar da manufar a bara ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin kashe tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 a bainar jama’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsaffin Kuɗi: SERAP ta maka Buhari, Malami, CBN Kotu
Wannan ya haifar da babbar muhawara. Bayan matsananciyar matsin lamba, babban bankin ya canza wa’adin da kwanaki 10.
Wasu gwamnonin jam’iyya mai mulki sun nemi shugaban kasar ya shiga tsakani, inda ya ce su ba shi kwanaki bakwai domin ya dauki mataki.
Sai dai bayan kwana uku da ganawa da Buhari, gwamnonin APC uku sun shigar da kara domin kalubalantar manufar sauya fasalin Naira a kotun koli.
Kotun ta umarci CBN da kada ya aiwatar da wa’adin amma Godwin Emefiele, gwamnan CBN, ya ce babu bukatar sauya wa’adin.
Buhari dai ya bi umarnin kotu a wani bangare bayan da ya bayar da umarnin tsawaita wa’adin amfani da Naira 200 tare da bayyana cewa tsofaffin takardun N500 da N1000 ba su da amfani.
Hakan ya jawo cece-kuce a fadin kasar. Gwamnonin jam’iyya mai mulki sun bi sahun masu sukar Buhari kan lamarin.
Yayin da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa manufar sake fasalin Naira na da nufin durkusar da dimokuradiyyar Najeriya ne, takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci mazauna yankin da su yi watsi da umarnin Buhari.
Gwamnonin Dapo Abidoun (Ogun), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abubakar Badaru (Jigawa) na daga cikin wadanda suka bayyana cewa har yanzu ana biyan tsofaffin takardun kudi na N500 da N1000 a jihohinsu.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwankwaso ya ce ya kadu matuka yadda gwamnonin APC za su iya yin hakan.
“A kowace jiha kana da rassan bankuna, a wasu jihohin ma, kana da hedkwatar wadancan bankunan na kasa, a bangare guda muna tunanin su (gwamnonin) za su karbi dukkan biliyoyin da ke gidajen gwamnati da sauransu.
“Amma mun fahimci wadannan gwamnonin suna zagin shugabanninsu, suna zaginsu, abin ya ba ni mamaki. Ban taba tunanin wasu daga cikinsu za su iya zagin Buhari har haka ba.
“A gefe guda na yi mamakin yadda bayanai ke fitowa sai muka fara tunanin me ke damun su? Watakila EFCC ta yi gaskiya cewa wasu gwamnoni suna ajiye biliyoyin nairori a gidajensu a fadin kasar nan.
A wani labarin kuma: Zaben Shugaban Kasa: Ba Zamu Taɓa Haɗa Kai Da PDP – Inji Al-Mustapha
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance don zaben 2023, Manjo Hamza Al-Mustapha (ritaya), ya yi watsi da rahotannin da ke cewa jam’iyyarsa ta amince da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
A babban taron yakin neman zaben Atiku da aka gudanar a Adamawa ranar Asabar, shugaban jam’iyyar APM na kasa, Yusuf Dantele, ya ce jam’iyyarsu da wasu mutane hudu sun amince da Atiku.