1 – Za’a kirkiro da ma’aikata da zata rika tattance wa’azzuka da kuma malaman da zasu rika yin wa’azi a fadin jihar.
2 – Kowane malami sai ya mallaki lasisin yin wa’azi, musulmine ko kirista.
3 – Za’a kafa irin wadannan Ofisoshi a kanan hukumomin jihar, wadda sune zasu rika Mika wa hukumar sunayen malamai da fastocin da Za’a tattance sannan kuma a basu lasisin yin wa’azi.
Duk wanda bashi da lasisin yin wa’azi zai ko ga tasko.
4 – Daga yanzu saidai ka saurari wa’azin ka acikin mota,gida, Cikin massallaci da dakuna. Wanda duk aka kama ya kure wa’azi yana saurare zai kuka da kansa.
5 – Duk wanda ya kure karatu ko wa’azi ta lasifika daga karfe 11 na dare zuwa karfe 4 na safe zaiyi kwanan kurkuku ko kuma ya biya taran naira 200,000.
6 – Sannan kuma duk wanda aka samu yana fadin kalaman batanci ga wani ko addini zai biya taran naira 100,000 ko kuma a garzaya da shi kurkuku ko kuma duka.