Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya yi barazanar cewa duk wanda ya yi kunnen uwar shegu kan umarnin haramta tuwita a Najeriya to zai san matsayinsa a gaban kuliya manta sabo.
Idan za a iya tunawa a ranar asabar ne Malami ya bada umarnin tusa keyar duk wanda aka cafke da bijirewa umarnin gwamnatin tarayya na haramta tuwitar.
Ko da yake cikin umarnin nasa na ranar asabar bai bayyana hukuncin da za a yi ba, amma a hirarsa da da yan jarida jiya Lahadi, ya bayyana cewa duk wanda aka kama to zai dandana kudarsa matuƙa.
Da yake magana da ta bakin mai tallafa masa Umar Gwandu, Malami ya bayyana cewa ba zai su ayyana irin hukuncin da za a yi ba, amma duk mai son sani to ya bijirewa umarnin haramta tuwitar domin an ce gani ya kori ji.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Juma’a ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin haramta ayyukan Tuwita a Najeriya biyo baya zarginsa da aka yi da ruruta wutar rikici a Najeriya.