Yayin da kai ke kara wayewa a duniya, a hannu guda kuma za a iya cewa wasu nasu kan kara dulmiyewa yake.
Wannan ya zo daidai lokacin da wasu mata ke kokarin shiga daga ciki ne ko ta halin ƙaƙa don samun gurin fakewa a yi zaman aure.
To sai dai bisa ga alamu dai matashiya Cynthia Uche Onuorah da ita ke hankoron ita ma ta samu wanda zai rufa mata asiri, ra’ayin ta ya sha banban da na saura mata musamman a Nigeria, domin ta gindaya wani sharadi nenda dole mijin da zai aure ta sai ya cika shi.
Cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na Facebook, Onuorah ta ce duk saurayin da ya Kudirin aniyar aurenta, to ya tabbata sai mahaifiyarsa ta bar duniya gabannin zuwa neman auren nata.
Ko da yake babu wani dalili da ya sa ta faɗi wannan kalamai, to amma sau da dama ana samun mata musamman na wannan zamani na nuna adawar su ƙarara da uwar miji, wacce har ake mata lakabi da ciwon kirji wato Ulcer.
Amma wannan mataki na Matashiya Cynthia Uche Onuorah bai yi wa mabiyanta na facebook ɗin daɗi ba, wanda ya har ya kai galibin mabiyan nata na mata kalaman Allah wadai, inda har wata daga cikin su mai suna Ekeocha Queen ta yi mata shaguɓe da cewa abinda ka yi dole a yi maka, don haka Onuorah ita shirya ma ranar ita ma surukarta za ta shigo.
To sai dai kawo wannan lokaci da muke haɗa muku wannan rahoto, Matashiyar mai suna Cynthia Uche Onuorah ta goge wancan rubutu da ta wallafa, duk da yake ba ta ƙara cewa uffan ba game da matakin nata.
Comments 1